20 Mayu 2020 - 07:18
Limamin Cocin Katolika A Kamaru Ya yi Iƙirarin Gano Maganin Cutar Korona

Rahotanni da suka fito daga kasar Kamaru sun nuna cewa wani Babban limamin cocin Katolika a birnin Duala da ke Jamhuriyar Kamaru, Samuel Clade, ya yi ikirarin cewa ya gano maganin gargajiya da zai warkar da cutar korona virus da ta Adabi duniya.

(ABNA24.com) Rahotanni da suka fito daga kasar Kamaru sun nuna cewa wani Babban limamin cocin Katolika a birnin Duala da ke Jamhuriyar Kamaru, Samuel Clade, ya yi ikirarin cewa ya gano maganin gargajiya da zai warkar da cutar korona virus da ta Adabi duniya.

Maganin da limamin cocin ya fito da shi ya fuskanci suka daga likitocin kasar inda suka nuna rashin ingancinsa saboda ba’a gwada shi ba.

Sai dai limamin Ya ce duk da bai rigaya ya sanya wa maganin suna ba, amma ya yi wa Alummar kasar alkawarin cewa zai bada da maganin kyauta ne ga jama'a idan ya fito da shi

Har ilayau ya yi wasti da sukar maganin da likitocin kasar suka yi da suka ce bashi da inganci, Samuel Claude ya ce ba"ruwansu ko su aminta da maganina ko su yi watsi da shi, shi dai zai fito da shi domin bai kamata a bari mutane suna mutuwa hakan nan ba,

Idan dai ba’a manta ba Hukumar Lafiya ta Duniya ta sha yin gargadi ga jama'a da su guji yin amfani da magungunan gargajiyar da wasu ke ikirarin ganowa da masana da likitoci ba su amince da shi ba saboda rashin yin gwaji akansa.



/129